Take a fresh look at your lifestyle.

FEC Ta Amince Da Dokar Kafa Hukumar Kula Da Cocoa Ta Kasa

70

Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kudirin kafa hukumar kula da koko ta kasa (NCMB) wanda ke nuni da wani babban mataki na farfado da masana’antar koko ta Najeriya.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa
ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa shirin na da nufin tabbatar da Najeriya a matsayin babbar jigo a kasuwar koko ta duniya tare da inganta jin dadin manoman koko a fadin kasar.

Wannan yunkurin ya yi daidai da manyan manufofi don tabbatar da ayyuka masu dorewa da inganta rayuwar kananan manoma wadanda ke da mahimmanci ga masana’antu.

Kyari ya kuma kara da cewa hukumar ta NCMB za ta ba su damar daidaita sashin koko gyara gonaki samar da lamuni mai sauki ga manoma da aiwatar da ka’idojin kasuwa.

Har’ila yau hukumar za ta bunkasa tattalin arzikin koko mai dorewa wanda zai ba da gudummawa sosai ga GDP Najeriya ta hanyar bunkasa amfani da cikin gida da jawo hankalin matasa zuwa harkar noma da kara samun kudaden musanya ta kasashen waje ta hanyar fitar da kayayyakin koko masu inganci zuwa kasashen waje.

Kyari ya ce ” a shekarar 2023 Najeriya ta samu Naira biliyan 356.16 daga waken Da koko da kayayyakin hadin gwiwa da wannan sabon tsarin za mu yi takara kai tsaye da manyan masu samar da kayayyaki na duniya kamar Ghana da Cote d’Ivoire” in ji Kyari.

Hukumar ta NCMB za ta kuma sa ido kan dabarun samarwa da masana’antu don tabbatar da wadatar da kwanciyar hankali a kasuwa. Da zarar an kafa shi hukumar za ta amince da aiwatar da duk ka’idojin aiki da kasuwa a cikin sarkar darajar koko.

Ministan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da mika kudirin ga majalisar dokokin kasar domin aiwatar da dokar.

Aisha.Yahaya, Lagos

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.